Home Taska Mabiya Addinai Biyu a Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniya

Mabiya Addinai Biyu a Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniya

Mabiya Addinai Biyu a Najeriya Sun Sanya
Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniya

 

Shugabannin addinin Musulunci da Kiristoci fiye da 50 ne suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu a Najeriya,

An ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya da za ta mayar da hankali wajen inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin addinai, a taron da ƙungiyar Musulmi ta Duniya da ke da hedikwata a Saudiyya ta shirya a Abuja.

Yarjejeniyar ta zo ne watanni bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Najeriya da gaza kare Kiristoci daga hare-haren ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, tare da yin barazanar daukar matakin soji kan ƙasar.

Sai dai ba a yi magana kan kalaman Trump ba a taron da aka sanya hannu kan yarjejeniyar.

Sakatare Janar na ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammad Al-Issa, yana cewa dukkanin mabiya addinan biyu na maraba da wannan tsari da ya ce ya “buɗe sabon shafi”.

Shugabannin Musulmi da Kiristocin da suka halarci taron sun ce yarjejeniyar za ta iya taimakawa wajen rage kalaman ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wajen bikin, ya ce gwamnati ta kuduri aniyar ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa duk da bambance-bambancen da ke tsakaninta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp