Home Taska ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 da Sace 16 Tsakanin 14 da...

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 da Sace 16 Tsakanin 14 da 19 ga Watan Maris a Jahar Kaduna – Nagwari

Raymond Dokpesi of AIT
Raymond Dokpesi of AIT

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 da Sace 16 Tsakanin 14 da 19 ga Watan Maris a Jahar Kaduna – Nagwari

An rahoto cewa yan bindiga sun kashe mutane biyar sannan suka yi garkuwa da wasu da dama.

Shugaban wata kungiya ta kula da harkokin tsaro da shugabanci na gari, Ibrahim Abubakar Nagwari, ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce lamarin ya afku ne a lokaci daban-daban a tsakanin ranar14 da 19 ga watan Maris.

Kaduna – Yan bindiga sun kashe mutane biyar ciki harda wani malamin makaranta a hanyar Layin Lasan Tabanni da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

An tattaro cewa yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane 16 a kauyukan Dogon Dawa, Layin Mahuta, da Tabanni da ke yankin gabashin karamar hukumar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar kula da harkokin tsaro da shugabanci na gari, Ibrahim Abubakar Nagwari.

Kungiyar ta ce lamarin ya afku ne a lokuta mabanbanta tsakanin 14 da 19 ga watan Maris, Daily Trust ta rahoto.

Kungiyar ta bayyana cewa a ranar 14 ga watan Maris, yan bindiga sun kashe wani Haruna Tanko Dogon Dawa da wasu mutane biyu a hanyar Dogon Dawa- Zaria.

Nagwari ya ce:

“An kuma yi garkuwa da wasu mutane takwas a wannan hanyar. A Layin Mahuta (Tabanni), an kashe wani Abdullahi Abubakar wanda yake malamin makaranta ne a hanyar Layin Lasan Tabanni a ranar 16 ga watan Maris.

“A ranar 17 ga watan Maris, an kashe wani tsoho dan shekara 70 sannan aka sace wasu mata bakwai a Layin Mahuta Tabanni. An kuma yi garkuwa da wasu biyu a tsohon Tabanni.”

Shugaban kungiyar ya kara da cewar a yankin Randagi, yan bindiga sun saki mutane 32 daga cikin 46 da suka sace a makonni uku da suka gabata a Unguwar Bula da Ijinga bayan an biya kudin fansa naira miliyan 16.

Ya bukaci jami’an tsaro da su dunga amsa kiran gaggawa a kewayen gudunmar Dogon Dawa, Kuyello, Tabanni, Kutemashi da Birnin Gwari, rahoton The Nation.

Sai dai kuma, shugabar karamar hukumar, Hajiya Ummah K. Ahmed, wacce ta tabbatar da kisan malamin da raunata wani, ta ce bata san da labarin sauran hare-haren da sace-sacen mutane da kungiyar ta ambata ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp