Harin da Rasha ta Kai wa Ukraine Yana Gudana Yadda Aka Tsara Shi Tun Farko – Minista Sergei Lavrov
Bayan tatatunawar da ministocin harkokin wajen Rasha da Ukraine suka yi kai tsaye a Turkiyya, minista Sergei Lavrov na Rasha ya amsa tambayoyi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Da aka tamabaye shi yadda yakin da kasarsa ke yi a Ukraine, ya ce harin aiki ne na musamman kuma yana gudana yadda aka tsara shi tun farko.
Lavrov ya tuhumi kasashen yammacin Turai da daukan matakai “masu hadari” ta hanyar ba Ukraine makamai, yana cewa wannan matakin ya keta “dukkan abubuwan da suka amince da su.”
Da aka tambaye shi ko Rasha na da niyyar kai wa wasu kasashen hari, sai ya ce ba ta da wannan shirin kuma ya nanata matsayar Rashar cewa ba hari ta kai wa Ukraine ba.











