Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago
Daga Hassana Magaji
Ana Zargin Wani Manomi Mai Suna Tafiya da Yiwa Wata Mata Mai Suna Hajjo Yankan Rago, Wanda Yayi Sanadiyyar Mutuwar ta Nan Take.
Lamarin dai Ya Aukune a Wani Gari da Ake kira Mabono dake Karamar Hukumar Bangi a Jihar Neja,Yayin Bincike Angano Cewar Mutumin Ya Yankata ne Sanadiyyar Shiga Gonan Gyadan shi da Dabbobinta Sukayi Inda Sukaci Wani Sashi na Gyadan daya Shuka.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Lamarin dai Ya Haifar da Cece Kuce Tsakanin ‘Yan Sanda Da Mutanen da Lamarin Ya Shafa Inda Dakyar da Sudin Goshi Suka Amince da Bayar da Gawan Hajjon Domin a Sallaci Gawar nata.
Har Yanxun dai ‘Yan Uwan Wanda Ake Zargi da Aikata Kisan Sunyi Dafifi a Harabar Ofishin ‘Yan Sandan Inda Suke Neman Abasu Belin Wanda ake Zargin, Yayinda Rundunar ‘Yan Sandan Sukayi Watsi da Bukatar ta su.
Tuni Angudanar da Jana’izar Marigayiyar Kamar Yadda Addinin Musulunci Ta Tanada,Sedai A dayan Bangaren ‘Yan Uwanta Nakira da Masu Ruwa da Tsaki dasu Gaggauta bi masu Hakkin Wannan Aika Aika.












