Home Labarai Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta cafke mutane 62 da ake zargi...

Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta cafke mutane 62 da ake zargi da aikata laifukan fashi da Makami a jihar

Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta cafke mutane 62 da ake zargi da aikata laifukan fashi da Makami, Sata da aikata Daba da kuma Dilolin ƙwaya da dai sauransu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar juma’a .

Sanarwar ta ce, an samu nasarar ƙwato muggan makamai guda 46 , sai codeine 253 , madarar Sukudayin 200 da kuma ƙulli-ƙulli na tabar wawi guda 1,802 da Babura biyu sa sauran muggan ƙwayoyi.

Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ya godewa al’ummar jahar bisa haɗin kai da goyon bayan sa suke bawa rundunar a koda yaushe.

Kiyawa ya ƙara da cewa, nasarar ra biyo bayan miƙa wuya da wasu matasa 99 suka yi sa ake zargi da aiyukan Faɗan Fada a cikin birnin Kano, waɗanda suka Tuba tare da ajiye makamansu.

Rundunar ƴan sandan jahar ta sanya tukwicin Naira dubu ɗari 300,000. ga dukkan wanda ya bauyar da bayanan sirri kan wasu matasa uku da suka ƙi miƙa wuya dan a cafke su.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 6 Sun Rasu 4 Sun Jilkata Sanadiyyar Tsawa a Jihar AdamawaMatatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man FeturZaɓen 2027: Jam'iyyar ADC ta Mayar da Martani kan Hukuncin Kotu Akwai Yiwuwar ba zan kai Lokacin Zaɓen 2027 ba - ObiHukuncin da Kotu ta Yanke wa Direban Keke Napep Kan Aikata Fyaɗeɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr Kurfi Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar TsaroGwamnatin Tarayya ba ta Yanke Hukuncin Sauya Kayan NYSC ba - Ministan MatasaJuyin Mulki: DSS ta Gurfanar da Mutane 5 kan ɓoye Timipre Sylva Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 Tare da Limami a Jihar Sokoto Dakarun Soji Sun Bankaɗo Wajen ƙera da Rarraba Bindigogi ga Ƴan Ta'addaJami'an DSS Sun Kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche NnajiYan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Jihar BenueNMDPRA ta Gargaɗi Gidajen Man da ba su Rage Farashi ba NECO: ɗalibai 35 na Hannun Ƴan Bindiga - Ƴan Sanda 
X whatsapp