Gwamantin habasha ta saka dokar ta baci ta watanni shidda a yankin Amhara, yanki na biyu mafi gima a kasar.
Wannan na zuwa ne biyo bayan wasu arangama da ake tsakanin dakarun sojin kasar da wasu gungun mayaka, abinda ya haifar da dakatar da zirga-zirga.
Rikicin daya barke a yanki a wannan mako, ya zama babbar barazana ga tsaron kasar shekaru biyu bayan rikicin yankin Tigray wadda ke makotaka da Amhara.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamantin yankin Amhara ta bukaci tallafin Karin jami’an tsaro daga gwamantin tarayyar kasar domin tabbatar da zaman lafiya.
Ta cikin wata sanarwa da ofishin friminista kasar Abiy Ahmad ya fitar yace, ya zame mana wajibi mu Sanya dokar ta bacin domin samar da tsaro kafin lamarin ya ta’azzara.
Habasha ce kasa ta biyu mafi yawan al’umma bayan Nijeriya, na fuskantar matsalar tashe-tashen hankula, tun bayan darewar Abiy Ahmad karagar mulkin kasar a shekarar 2018, duk da cewa ya sami lambar yabo ta zaman lafiya a shekarar 2019 bisa gudunmawar daya bayar wajen samar da zaman lafiya a kasar Eritrea.
PRNigeria hausa











