Home AFIRKA Rashawa na janyo wa Uganda asarar sama da dala biliyan 2 duk...

Rashawa na janyo wa Uganda asarar sama da dala biliyan 2 duk shekara

Uganda na yin asarar kuɗin da ya kai Dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 500 a duk shekara saboda cin hancin, kwatankwacin kaso 1 bisa 4 na kasafin kuɗin da ƙasar ke yi, kamar yadda hukumar da ke yaƙar cin hanci a  ƙasar ta tabbatar.

A cewar shugabar hukumar yaƙi da cin hanci ta Uganda Beti Kamya Turwomwe, ƙasar na asarar sama da tiriliyan 9 da miliyan 100 na kuɗin ƙasar Shiling, kwatankwacin dala biliyan 2 da miliyan 500 a duk shekara.

Ta ce wannan ya kai kaso 23 cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar, abin da ke zama wani babban ƙalubale ga ayyukan daƙile cin hanci a ƙasar.

Cin hanci da rashawa wata gagarumar matsala ce da ke addabar gabashin Afirka.

Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Musaveni ya sha nanata alwashin ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar cin hanci ganin yadda matsalar ta ratsa cikin jami’an gwamnati.

Turwomwe ta ce sashin da ta ke jagoranta ya samu nasrar ƙwato dala miliyan 2 da aka wawushe, inda ta nuna damuwa kan rashin sanya kuɗi a hukumar da take jagoranta.

Wannan kalaman nata ya biyo bayan rahoton shekara-shekara da ake fitarwa na cibiyar bincike kan tabbbatar da ganin an yi ayyukan gwamnati a buɗe babu kumbiya-kumbiya.

Rahoton na zuwa mako guda da shugaban Uganda Yoweri Musaveni ya sanar da yafewa wasu manyan jami’an gwamnati da aka ɗaue shekara 10 saboda kamasu da badaƙalar dala miliyan 1 da miliyan 200.

Musaveni ya yafe musu bayan sun kammala shekara 5 a gidan 5, abinda ya tunzura kungiyoyin fararan hula

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp