Adadin Matasa ‘Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 – NDLEA
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA Buba Marwa ya ce sama da kashi 60 na masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da suka kama cikin shekaru biyar da suka ggabata matasa ne.
Adadin mutanen da aka kama ya kai 77,859, wanda haka ke nuni da ta’azzarar ta’ammali miyagun kwayoyi tsakanin matasa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Marwa ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da maƙala kaso na 29 zuwa 30 a jami’ar Abuja, wadda ta zama Jami’ar Yakubu Gowon, kamar yadda sanarwar da Femi Babafemi daraktan yaɗa labaran hukumar ya fitar.
Ya gargaɗi matasan Najeriya musamman waɗanda suke makarantun gaba da sakandire, saboda shaye-shayen yana kassara rayuwar matasan Najeriya da ya kamata su zama masu amfani ga ƙasar.
Ya ce harkar shaye-shaye ta bar kan titunan Najeriya ta koma cikin makarantu.












