Home Taska An Kama Mai Taimakawa ‘Yan Kungiyar Lakurawa Wajen Samun Kudi a Jihar...

An Kama Mai Taimakawa ‘Yan Kungiyar Lakurawa Wajen Samun Kudi a Jihar Sokoto

Police-Arrest

An Kama Mai Taimakawa ‘Yan Kungiyar Lakurawa Wajen Samun Kudi a Jihar Sokoto

 

Jihar Sokoto, Nigeria – Rundunar ‘yan sandan Sokoto ta sanar da cafke wasu da ake zargi da ba ‘yan bindiga bayanai da kuma taimaka masu wajen samun kudade.

Kwamishinan ‘yan sanda na Sokoto, Hayatu Hassan Shaffa, ya ce a ranar 17 ga Afrilu, 2026, jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane sun kama wani Aminu Mai Roba daga kauyen Maikulki da ke karamar hukumar Binji.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa da yake hira da manema labarai, ya ce an tare wanda ake zargin ne a kan hanyar Ruwa-Wuri zuwa Tangaza dauke da shanu guda hudu.

An samu bayanai daga bakin mutumin

A cewar CP Hayatu, bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya karbi shanun ne daga kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa a kauyen Wariya da ke Tangaza.

“Ya bayyana cewa aikinsa shi ne sayar da shanun sannan ya mayar da kudin ga kungiyar ‘yan ta’addan. Mun fara hada hujjoji yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.” in ji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce wannan na daga cikin kokarin rundunar wajen tabbatar da gaskiya da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da al’umma

Ya jaddada cewa rundunar na ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da dakile aikata laifuka, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Jami’an tsaro sun fatattaki yan bindiga

Ya kuma bayyana cewa a ranar 8 ga Afrilu, da misalin karfe 4:20 na safe, ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa kan harin da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Kwarengamba da Gayya da Kwari a karamar hukumar Sabon Birni

A cewarsa, jami’an ‘yan sanda tare da sojoji, ‘yan sa-kai da masu tsaron al’umma sun kai dauki cikin gaggawa.

Ya ce hadakar jami’an tsaron ta fafata da ‘yan bindigar inda aka fatattake su bayan musayar wuta mai tsanani.

“Maharan sun tsere da raunukan harbi zuwa cikin daji, sannan suka bar buhu dauke da harsasai 167,” in ji shi.

Kwamishinan ya yaba da kokarin jami’an tsaro, yana mai cewa nasarorin da aka samu na nuna kwarewa da jarumtaka, tare da karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro daban-daban da al’umma baki daya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp