Home SIYASA 2027: Jam’iyyun Adawa Sun Sanar da Shirinsu na Yakar Tinubu da APC

2027: Jam’iyyun Adawa Sun Sanar da Shirinsu na Yakar Tinubu da APC

Atiku

2027: Jam’iyyun Adawa Sun Sanar da Shirinsu na Yakar Tinubu da APC

 

Birnin Ibadan, jihar Oyo – Jam’iyyun adawa sun sanar da shirinsu na fafatawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.

Jam’iyyun adawar sun bayyana shirinsu na gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya tilo domin zaɓen shekarar 2027.

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa jam’iyyun adawar sun amince da wannan matsayar ne a ranar Asabar, 25 ga watan Afirilun 2026.

‘Yan adawa sun yi taro a Ibadan

An cimma matsayar ne yayin babban taron shugabannin jam’iyyun adawa na ƙasa da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Jaridar Vanguard ta ce an bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan babban taron da jam’iyyun adawar suka gudanar.

Manyan jiga-jigan adawa da suka haɗa da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Rotimi Amaechi, Peter Obi da Rauf Aregbesola, sun halarci taron.

‘Yan adawa za su yaki Tinubu da APC

Yayin da yake karanta sanarwar, shugaban wani ɓangare na jam’iyyar PDP, Taminu Turaki, ya ce bayyana cewa:

“Za mu bijire wa duk wata makirci na APC na son mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya tilo, kuma za mu yi yaƙi domin dorewar tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a ƙasarmu.”

Game da zaɓen 2027, ‘yan adawar sun yi watsi da iƙirarin cewa an riga an san sakamakon zaɓen, inda suka bayyana cewa:

“Duk da dabarun jam’iyya mai mulki, za mu fitar da ’yan takara kuma mu fafata a zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓukan 2027.”

An cimma matsaya kan fitar da dan takara Jam’iyyun adawar sun kuma bayyana shirinsu na tsayawa takara a ƙarƙashin inuwa ɗaya, inda suka ce:

“Za mu yi aiki wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya na zaɓen 2027, wanda dukkan jam’iyyun adawa da ke halartar taron za su amince da shi tare da ba shi goyon baya domin ceto al’ummarmu da suka daɗe suna shan wahala.”

Dangane da fargaba game da hukumar zaɓen, sanarwar ta bayyana cewa:

“Shugaban hukumar INEC, Joash Ojo Amupitan, tun da ya nuna son zuciya da nuna goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki, bai kamata ya gudanar da babban zaɓen 2027 ba.”

Sun soki tsare jiga-jigan ‘yan adawa Haka kuma sanarwar ta taɓo batun zargin danne haƙƙin siyasa, inda ta ce:

“Dukkan manyan ’yan siyasa da ake tsare da su ko ake muzantawa kan laifuffukan da za a iya bayar da belinsu, a sake su nan take kuma a ba su damar amfani da haƙƙinsu na ’yan ƙasa wajen shiga harkokin siyasa ba tare da nuna bambanci ba.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Tinubu ya Mika Dokoki Biyar ga Majalisar Dattawa Kan Gyaran Hukumar NDLEA, Tsaron Sufuri, da Laifukan YakiTunawa da NIPSS: Lambar Yabo ba Tare fa Hikima ba - Hannatu BilyaminuMataƙin Kano Ya Kammala Tseren Ɗinki na Sa'o'i 120 a Kokarin Kafa Tarihin Duniya na Guinness 2027: Dalilin da ya sa Aka Cire Wasu Ƴan Takarar Gwamna Daga Jerin Karshe - INECTunawa da NIPSS: Lokacin da Ka'ida ta Haɗu da Ƙarfi Daga Muhammad Inuwa IbrahimSa'o'i Bayan An Zaɓe Shi a Matsayin Sabon Jarumin Kamfen na APC, Gwamnan Jam'iyyar Accord ya yi Alkawarin Kuri'u Miliyan 1.5 ga TinubuEl-Rufai Ya Kasafta Dala Dubu 600,000 Domin Baiwa Jami'an EFCC, Shaidan DSS Ya Faɗawa KotuAn Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027
X whatsapp