‘Yan Siyasa ba sa yi wa Talakawan da Suke Jagoranta Adalci – Sanata Ningi
Sanata Abdul Ahmed Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya ce ‘yan siyasa ba sa yi wa talakawan da suke jagoranta adalci da yau ba a tsinci kai inda ake ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanata Ningi ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce lokutan kamfe ‘yan siyasa na shiga lungu da saƙo domin neman ƙuri’un talakawa, amma da zarar sun ci zaɓe ba sa komawa domin sanin halin da talakawan ke ciki.
“Ana ta kashe talakawan da muke wakilta, amma babu abin da yake gabanmu a yanzu sai lamuran zaɓe da siyasa”, in ji Sanata Ningi.
Ya ce a kullum sai ka ji rahoton kashe mutane a sassan arewacin Najeriya, kamar wadanda ba su da shugabanni.
“Shi yasa muka nemi majalisa ta sa a dakatar a dakatar da harkokin siyasa a jihohi 8 na arewa da suka fi shiga wannan matsala har sai an shawo kan matsalar,”.












