Home Taska Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu...

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar Mutane

DCP Anthony Okon Placid

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar Mutane

 

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta tarwatsa wata ƙungiyar masu safarar mutane da ke gudanar da ayyukanta a Abuja, babban birnin ƙasar da wasu yankuna maƙwabta.

Hakan ya sa ƴansanda suka kuɓutar da mutum 30 ƴan asalin Mali da ake zargin an tsare su a jihar Nassarawa.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Anthony Placid ya fitar, jami’an sun bankaɗo wasu ayyukan ƙungiyar a wani gida da ke Mararraba da Karu inda ake zargin an killace su.

Ƴansanda sun ce an kama mutum 13 da ake zargi suna da hannu a ƙungiyar.

A cewar ƴansanda, an soma bincike ne bayan da aka samu bayanan sirri kan ɓacewar baƙi da dama a Najeriya.

Placid ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar tana yaudarar matasa daga ƙasashe irinsu Mali da Gabon inda suke yi musu alƙawarin ayyukan yi a Najeriya da kuma damar tsallakawa zuwa Turai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp