Home SIYASA An faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi...

An faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi – Shettima

Shettima

An faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi – Shettima

 

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya bayyana yadda ya ce wasu suka yi ƙoƙarin haɗa shi da shugaban ƙasa Bola Tinubu, wata uku bayan fara mulkinsu.

Yayin da yake jawabi a wani taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban ƙasar, Janar Yakubu Gowon a Abuja, babban birnin ƙasar, Shettima ya ce wasu mutane da bai ambaci sunayensu ba, waɗanda ya ce daga jiharsa ta Borno suke sun faɗa Shugaba Tinubu cewa Shettiman na kitsa kashe shi domin karɓar mulki.

“Bayan wata uku da kama mulkinmu, wasu mutane suka faɗa wa Tinubu cewa ina kitsa yadda zan kashe shi domin na karɓi mulkin ƙasar. Daga nan sai ya kirani ya ce zauna mutanenka sun zo sun faɗa min cewa na daina saka tufafin da Shettima ya bani.”

“Sai dai da kansa Shugaba Tinubun ya ce min bai yarda da labarin nasu ba, saboda lokacin da ka bani tufafin ina matsayin ɗantakara ne, ban ma ci zaɓen fitar da gwani ba, ballanta ka zama mataimakin shugaban ƙasa”, in ji shi.

Ya ce wasu mutanen sun faɗa wa Tinubun cewa ina shirin amfani da tufafiun domin kashe shi.

”Kuma Shugaban ya saka tufafin bayan hakan saboda bai yi imani da hakan ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp