Home WASANNI NPFL: Kungiyar Kano Pillars zata Dawo Buga Wasa Jihar Kano

NPFL: Kungiyar Kano Pillars zata Dawo Buga Wasa Jihar Kano

Hukumar kula da gasar firimiya ta Najeriya, Nigeria Professional Football League (NPFL), ta bai wa ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars damar ci gaba da buga wasanni a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano.

Wannan dai na cikin Wata sanarwa da hukumar ta aike wa kungiyar ta kano Pillars, inda  ta ce yanzu haka kungiyar nada damar buga wasannin a filin bayan duba na tsanaki da hukumar tayi.

Ta cikin sanarwar Hukumar ta ce wajibi ne kungiyar ta kano Pillars ta tanadi wani filin wasan da za ta ci gaba da buga wasanni da zarar an fara aikin gyara ciyawar filin taka leda ta filin kafin kammala shi.

Tuni kungiyar kwallon kafar ta kano Pillars ta amince da sharaɗin, har, inda tace za ta buga wasanta na gaba tare da kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a Kano ranar 16 ga watan Afrilu.

Idan dai za’a iya tunawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ba ta buga wasa a gida ba a kakar bana sakamakon matakin da hukumar ta NPFL ta ɗauka, inda ta umarci a sauya ciyawar filin taka ledar.

Yanzu haka dai kungiyar ta Pillars na mataki na 13 da maki 26 bayan buga wasa 22 a kakar bana ta 2022/2023.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp