Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da kawo karshen barkewar cutar kwalara data addabi jihar.
Wannan ya fito ne ta bakin Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Isa Abdullahi, yayin da yake ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Yola Babban Birnin Jihar, inda yace cutar ta Kwalara ta barke ne a watan Yulin 2021, inda wata na gaba mutum 1,959 ake zargin sun kamu da cutar.
Ya zuwa ranar Alhamis, an sanar da kawo karshen barkewar cutar, wacce ta kama akalla mutum dubu biyu tayi sanadiyyar mutuwar mutane 55 a fadin jihar.
Read Also:
“Tun da bamu sami rahoton bullar cutar kwalara ba, bayan sanya idanu da mukayi na tsawon makwannin Gwamanti da Abokan huldar ta, muna farin cikin sanar da cewa yanzu hakan babu cutar kwalara a jihar Adamawa.
Sai dai kwamishinan yace bayyana kawo karshen cutar ta kwalara, ba wai wata dama bace da al’umma zasu yi amfani da ita ba wajen shakatawa tare da yin watsi da dokokin da masana kiwon lafiya suka gindaya kan cutar.
Kawai wannan wata kofa ce ga mahukunta domin sake zage dantse wajen inganta shirye-shiryen magance dukkan cututtukan dake yaduwa, wajen samar da rigakafin su.
Daga bisani ya mika godiyar su ga Hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma Asusu tallafawa kananan ya rana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da dukkan wadanda suka hada hannu da gwamnatin jihar tun daga watan Yuli har kawo yanzu da yawan masu kamuwa da cutar ya ragu matuka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 39 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 20 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com