Masu fama da ciwon Koda a jihar Kano dake Arewacin Nijeriya na kara shiga cikin hadari sakamakon rashin isassun injinan wankin kodar domin kula da masu fama da ciwon, inji rahoton bincike da PRNigeria ta gudanar.
Wani bincike da PRNigeri ta gudanr a baya-bayannan ya tabbatar da cewa cutar Koda (CKD) na ci gaba da karuwa a jihar Kano, ya kuma nuna cewa sama da majinyatan dake fama da cutar 200 a jihar sun dogara ne da injinan wankin kodar guda 12 kacal a manyan Asibitocin jihar da suka hadar da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), da Asibitin kwararru na Abdullahi Wase.
Binciken ya nuna cewa, akalla majinyata 160 da ke fama da ciwon kodar ke ziyartar asibitin kwararru na Abdullahi wase duk mako. Har ila yau, akwai sabbin majinyata 15 da ke zuwa don yin wankin koda ko wanne mako.
A yayin da a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano inda ake samun majinyata kusan 70 dake bukatar wankin kodar, Amma a cikin makon akalla mutum 40 kan jira domin yi musu wankin.
Duk da tsadar da magungunnan da masu fama da wannan lalura ke da shi, PRNigeria ta bankado cewa da yawa daga cikin Na’ororin wankin kodar a manyan cibiyoyin lura da masu fama da lalurar guda 2 dake jihar Kano basa aiki.
Bincike na PRNigeria ya kuma nuna cewa a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, injinin wankin kodar guda 8 ne kawai ke aiki a halin yanzu, kuma da yawa daga cikin masu fama da cutar suna jiran sama da sa’oi 10 kafin a yi musu wankin.
Aliyu Abdullahi, Farfesa a fannin likitancin Kodar dake jami’ar Bayero a jihar Kano, haka kuma shugaban sashin kula da cutar na Asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya ce abu ne mai matukar wahalar gaske a iya jure aiki da injinan wankin kodar da majinya da dama ke zaman jira domin ayi musu magani.
Read Also:
“A da muna da injinan wankin kodar har guda 20, amma saboda rashin isassun kudade da sauran kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu bamu da injina sama da 5 da ake aikin da su.
“Yana da matukar wahala a iya jurewa. Za ku ga marasa lafiya suna yin layin na awannin 10 ko 15 don samun wankin Kodar saboda lokacin da kuka sanya majinyaci a kan injin wanki, dole ne ya zauna na akalla sa’oi 4, sannan kuma kuna bukatar Karin sa’a 1 don tsaftacewa da kashe kwayoyin cutar daga kan injin kafin a shirya don majinyaci na gaba. Don haka zaku iya gani a rana daya, ba za ku iya dora marasa lafiya sama da guda 3 a kan na’ura guda ba.”
A Asibitin kwararru na Abdullahi Wase, wanda ake kallo matsayin asibitin mafi arahar cibiyar lura da masu fama da lalurar kodar a Kano, hudu (4) ne kadai daga cikin injina shidan (6) da ake dasu ke aiki.
PRNigeria ta tattaro cewa ana gudanar da duk maganin kodar cikin farashi mai sauki sakamakon, tallafin da Gwamnatin jihar ke bayarwa, amma duk da haka, ana kara ganin adadin masu fama da wannan lalura dake jiran wankin na karuwa a sashen.
Mukaddashin shugaban sashen masu fama da cutar Koda a Asibitin kwararru na Abdullahi Wase, Dakta Usman Adamu, Yace maganin cutar nada araha sosai domin farko naira dubu 15,000 ake saya sannan kuma naira dubu 8,000, kowannensu yana da araha idan aka kwatanta da sauran cibiyoyi.
“A nan muna da injinan wankin kodar kusan guda hudu, ana gab da gyara guda biyu. Hakazalika, a wannan asibiti muna samun matsakaicin adadin marasa lafiya 60 zuwa 80 a kowanne asibitin da kuma masu fama da cututtukan dake da alaka da koda, kuma daga cikinsu akwai da dama dake bukatar wankin kodar, sannan akalla akan sami sabbin majinyata 15 da ke zuwa domin yin wanki a wanna asibiti”.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 57 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 39 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com