Makiyaya sun hallaka mutane sama da dubu 5 a jihar Benue – BSEMA

Wani rahoto da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Benewai (BSEMA) ta fitar ya bayyana cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun hallaka kimanin mutane 5,138 a wasu kauyukan jihar tun daga shekarar 2015.

Babban sakataren hukumar, Dakta Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a garin Makurdi yayin da yake ganawa da manema labarai, ya kuma yi zargin cewa wasu mutane dubu 3 sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren da makiyayan suka kai a kwanakin baya a kananan hukumomin Gwer ta yamma, Logo, Ukum da kwande yayin da suka murna bisa faduwar da gwamnan Samuel Ortom jihar yayi a takarar sanata.

Ya ce a kalla kananan hukumomi 18 cikin 23 dake jihar makiyayan suka yiwa kawanya tare da kone gidaje, abinda ya jefa mutane miliyan 2 cikin halin rashin matsugunni.

Shugaban hukumar ta BSEMA yace ya karanta a jaridu cewa kungiyar Fulani na Shirin daukar wasu matakan akan jihar, inda yace yana mai bayyana fatan cewa gwamnatin Benuwai ba za ta yi kasa a gwiwa ba saboda rashin goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Titus Uba, ba zai  sauya matakin da Gwamna Samuel Ortom ya yi na tallafawa ‘yan gudun hijira a jihar ba.

Shior ya dage cewa sama da ‘yan gudun hijirar Kamaru 10,000 a karamar hukumar Kwande da ke jihar suna samun kariya daga jami’an sa kai na al’ummar jihar Benuwe daga farmakin makiyaya.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 22 hours 6 minutes 52 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 48 minutes 17 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com