Jam’iyyar Labour Party a jihar kwara ta dakatar da dan takarar dake mata takarar Gwamna a jihar Comrade Basambo Abubakar bisa zargin yunkurin cin amanar jam’iyyar wato Anty Party.
Shugaban jam’iyyar na jihar Chief Kehinde Rotimi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a illorin, inda ya ayyana dakatarwar ta sai baba ta gani, bisa zargin da ake masa na yin anty party tare da yada labaran kanzon kurege akan jam’iyyar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
In jiyo Basambo yayin da yake ganawa da manema labarai a Ilorin ranar litinin yana cewa jam’iyyar PDP ta LP a jihar kwara sun hade domin yin aiki wuri guda a zaben gwamna da na ‘yan majlisar jiha dake tafe a jihar.
Sai dai shugaban jam’iyyar ta LP dake karanta takaradar dakatarwar da jam’iyar tayi wa dan takarar Gwamnan yace kalaman say ace karo da matsayar jam’iyyar, haka kuma basi da hurumin yanke hukunci kan jam’iyyar a radin kan sa.
PRNigeria












