Jihohi 14 da zasu fuskanci Ambaliyar Ruwa a Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwar hasashen ambaliya a shekara ta 2023, inda ta ce jihohi 14 da al’ummomi 31 za su iya ganin ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da muhalli ta tarayya ta fitar.

A cewar sanarwar, an gano jihohin da al’ummomin da suka hada da:

Plateau – Langtang, Shendam

Kano – Sumaila, Tudun Wada

Sokoto – Shagari, Goronyo da Silame

Delta – Okwe

Kaduna – Kachia

Akwa Ibom – Upenekang

Adamawa – Mubi, Demsa, Song, Mayo-Belwa, Jimeta, Yola

Katsina – Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa

Kebbi – Wara, Yelwa da Gwandu

Zamfara – Shinkafi, Gummi

Borno – Briyel

Jigawa – Gwaram

Kwara – Jebba

Niger – Mashegu, Kontagora

Gwamnatin ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin kiyaye asarar rayuka da dukiyoyi.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 49 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 30 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com