Home Labarai Majalisar wakilai ta dakatar da JAMB daga hukunta yarinyar da ‘ta ƙara...

Majalisar wakilai ta dakatar da JAMB daga hukunta yarinyar da ‘ta ƙara wa kanta maki’

Majalisar wakilai ta Najeriya ta tsoma baki cikin batun zargin da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ta yi wa wata daliba mai suna Mmesoma Ejikeme na kirkirar sakamakon jarabawa na bogi wanda hukumar ta shirya na shekarar 2023.

‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda hukumar jarabawar ta gaza nuna dattaku kan lamarin da ya shafi karamar yarinya ta hanyar janye sakamakon jarabawarta tare da dakatar da ita na tsawon shekaru uku.

Sun ce yana yiwuwa akwai hannun wani a cikin lamarin.

Daga nan ne majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da neman hukumar JAMB da ta dakatar da zartar da hukunci har sai majalisar ta kammala bincikenta.

A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar ta JAMB ta zargi dalibar da kirkirar sakamakon bogi a jarabawar ta bana.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga PantamiGazawar Demarketing: Yadda Sukar Rarara Mai Cike da Kiyayya ga Pantami Ya Rushe Daga Yushau A. ShuaibƘungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin AikiDakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da suƳan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari'a da ke Jihar KatsinaBa ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe - INEC
X whatsapp