Ministan shari’a na Najeriya Lateef Fagbemi ya ce yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar suka fara a ranar litinin kan mafi ƙanƙantar albashi ya saɓa wa doka.
Babban lauyan na gwamnati ya bayyana hakan ne bisa dalilin cewa ƙungiyoyin ba su bi ka’idojin da dokar ƙwadago ta gindaya ba.
wannan dai na zuwa ne bayan manyan kungiyoyin ma’aikata biyu na NLC da TUC, suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga Litinin bayan gwamnati ta gaza cika wa’adin ranar 31 ga watan Mayu na aiwatar da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta da kuma rage farashin wutar lantarki.
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta NLC da TUC sun ce za a fara yajin aikin har sai sun sami sabon albashi mafi ƙanƙanta na ƙasa kuma har sai gwamnati ta yi da gaske.
Ƙungiyoyin ƙwadagon na son a sanya albashi mafi ƙanƙanta kan dala $334, kwatankwacin N494,000 kenan inda kuma gwamnati ta tsaya a kan Naira 30,000, kwatankwacin dala 22, duk wata.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 4 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 45 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com