Jagoran jam’iyyar adawa ta LP a Najeriya, Peter Obi ya yi kira ga mahukuntar ƙasar, musamman ministan shari’a da rundunar ‘yansanda da DSS da kuma hukumar kare haƙƙin bil-adama su gudanar da cikakken bincike kan ”azabtarwar da aka yi wa ƙananan yaran da aka gurfanar a gaban kotu bisa zargin cin amanar ƙasa.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Obi ya ce bidiyon yaran da aka yaɗa a gaban kotu abin tayar da hankali ne.
”Halin da yaran ke ciki na yunwa da galabaita abin tayar da hankali ne ga duk wani mai hankali a ƙasar nan”, in ji shi.
A yau ne dai ‘yansandan Najeriya suka gabatar da wasu mutane ciki har da ƙananan yara a gaban kotu bisa zargin laifuka masu yawa ciki har da cin amanar ƙasa, kimanin wata uku bayan kamasu.
Yadda aka gabatar da yaran ya janyo ka-ce-na-ce a faɗin ƙasar, musamman yadda aka ga wasu daga cikin ƙananna yaran cikin mawuyacin hali.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 52 minutes 8 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 33 minutes 33 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com