A yau Litinin ne za a fara allurar riga-kafin ƙyandar biri a wasu jihohi bakwai a Najeriya., wanda hakan zai sa ƙasar ta zama ta uku da za ta yi riga-kafin bayan Rwanda da Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya za ta yi riga-kafin a kan cutar ta ƙyandar biri bayan ɓarkewarta.
Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta ce za a fi mayar da hankali ne a kan ma’iakatan lafiya da sauran rukunan jama’a da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Read Also:
A watan Agusta Najeriya ta karɓi allurarn riga-kafin na farko da aka bai wa Afirka, wanda kuma a wannan watan ne hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar a matsayin annoba ta duniya
Amurka ta bai wa Najeriya kwalaban allurar sanfurin Jynneos (MVA), 10,000.
Tun daga farkon shekarar nan rahotanni sun tabbatar da mutum 118 a jihohi 28 daga cikin 36, da kuma Abuja. ne suka kamu da cutar a Najeriya, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta sanar.
Hukumar yaki da bazuwar cutuka ta Najeriya ta ce, zuwa yanzu a wannan shekara daga watan Oktoba, 27, akwai mutane 1,442 da ake zargin sun kamu da cutar daga jihohi 36 da kuma Abuja.
Kasashen Afirka 20 sun tabbatar da bullar cutar a kasarsu a wannan shekara, kuma aranar Asabar ne Angola ta bayar da rahoton mutum na farko da ta tabbatar ya kamu a kasarta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1250 days 44 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1232 days 2 hours 26 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com