Matatar man Ɗangote ta ƙara farashin man fetur da naira 100

Matatar Man Ɗangote ta sanar da ƙarin farashin naira 100 kan kowacce litar man fetur guda inda a yanzu ta sanar da cewa za ta koma sayar da man akan farashinj naira 799.

Tun daga ranar 12 ga watan Disamban bara matatar ke sayar da kowacce litar man guda kan farashin naira 699 sai dai a wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, ta ce farashin ya sauya nan ta ke.

Sanarwar matatar ta ce gidajen manta na MRS za su koma sayar da kowacce lita guda a farashin naira 839 daga naira 739 da suke sayarwa a baya.

Sanarwar ta Ɗangote ta ce tun farko an zaftare farashin ne saboda bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara, kuma bayan ƙarƙarewar wannan bukukuwa farashin zai dawo yadda ya ke a baya.

Matatar ta jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tuƙuri wajen daidaita farashin man tare da tabbatar da wadatuwarsa a sassan ƙasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com