Home Taska Jihohin da Zasu fi Fuskantar Matsanancin Yanayin Zafi – NiMet

Jihohin da Zasu fi Fuskantar Matsanancin Yanayin Zafi – NiMet

NiMet

Jihohin da Zasu fi Fuskantar Matsanancin Yanayin Zafi – NiMet

 

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargaɗin cewa za a samu matsanancin yanayin zafi a ƙasar, inda ta ce hakan zai iya kai wasu ga shiga yanayin galabaita saboda zafin a wasu sassan ƙasar.

A wata sanarwa da ta fitar a shafukanta, NiMet ta ce yanayin zafin zai fi shafar jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da jihohin Neja da Kebbi da Kano da Sokoto da Zamfara da Katsina da Yobe da Jigawa da Bauchi da Gombe da Borno da kuma Adamawa.

A cewar sanarwar, akwai yiwuwar wasu jihohin ma da ba a ambata ba su samu ƙaruwar yanayin na zafi.

A hasashen ta, yanayin zafin zai iya kai wa maki 40 zuwa 45 a ma’aunin salshiyas a arewacin ƙasar, yayin da tsakiyar ƙasar kuma zai kai tsakanin maki 35 zuwa 38 a ma’aunin salshiyas, a Kudancin ƙasar kuma yanayin na iya kai wa maki 33 zuwa 35.

Hukumar yanayin ta buƙaci alumma su riƙa shan ruwa sosai, sannan su kasance a wuri mai iska sosai tare da kaucewa wurare masu cinkoson alumma, kuma su rage zama ƙarƙashin rana.

Ta kuma shawarce su da su sanya hula da gilashi idan za su fita, kuma su sanya kaya marasa nauyi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp