Home Taska Hukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar Neja

Hukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar Neja

Hukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar Neja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum biyar hukuncin daurin shekara 25 kowannensu bayan samunsu da laifin taimakawa ayyukan ta’addanci da ke da alaƙa da sace ɗalibai.

Harin wanda aka kai makarantar St. Joseph Catholic Church da ke Papiri a Jihar Niger.

A harin da aka kai ranar 21 ga Nuwamban 2025, maharan sun sace ɗalibai da ma’aikata sama da 300. Duk da cewa wasu kusan 50 sun tsere, an yi awon gaba da sama da ɗalibai 250 zuwa dajin Kainji.

Hukumar Tsaro ta DSS ta bi sawun wasu daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a lamarin tare da cafke su.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai ’yan Najeriya da kuma ’yan Jamhuriyar Nijar biyu.

A lokacin kamen, jami’an DSS sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-103 guda 15 da harsasai 1,434 da aka ɓoye a cikin buhuna a wata mota kirar volkswagen Golf.

Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin bayan mutanen biyar sun amsa laifuffukan da ake tuhumarsu da su, waɗanda suka haɗa da: haɗa baki da kuma taimakawa ayyukan ta’addanci ta hanyar safarar makamai ga wani da ake zargin mamba ne na Boko Haram.

Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace motar da aka samu makaman a cikinta tare da mayar da ita mallakin gwamnatin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Farashin ɗanyen Mai ya Faɗi Bayan Amurka ta Soke Sabbin Hare-Haren kaiwa IranAmurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran - TrumpMajalisar Wakilan Najeriya ta Amince da ƙudirin Dokar Kafa ’Yan sandan JihaHukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar NejaMiyagun ƙwayoyi da Makamai: Jami'an Tsaro Sun Kama Mutane 8 a Jihar YobeAbin da Obi ya Fada Kan Atiku - Dele MomoduHukumar EFCC ta Gurfanar da Ma'aurata Kan Damfarar Kudi Kusan N2bnFiye da Kashi 60 na 'Yan Najeriya a Yanzu Suna Rayuwa Cikiin Fatara - IMFGwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasartaƳan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a ZamfaraMayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar Gombe
X whatsapp