Amurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran – Trump
Da yake magana a fadar White House, Trump ya ce “Amurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran “.
Ya ci gaba da cewa: “Muna kan kammala tattara takardun yarjejeniyar. Za iya kamatawa nan da ƴan kwanaki masu zuwa.”
Trump ya ce “wataƙila za a sanya hannu, mai yiwuwa a Turai” da zarar an kammala tattara takardun, kuma ya kamata a yi “da sauri”.
Read Also:
“Mun ƙulla yarjejeniyar cewa Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba, wanda shi ne maƙasudin abin da ya sa muka yi wannan abun don mu samu hakan. Don haka abu ne babba.”
Trump ya ce za a buɗe mashigar Hormuz “da zarar mun sanya hannu”.
Ya kuma ce ya yi magana da shugabannin yankin da suka haɗa da ƙawayen Amurka na ƙasashen Gulf da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ƙara da cewa: ” Yankin Gabas ta tsakiya baki ɗayanta na mauƙar farin ciki”.










