Home Labarai Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin...

Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?

Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?

 

Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, har yanzu cece-kucen da suka biyo bayan matakin ba su lafa ba.

Gwamnatin Jihar Osun ta nuna adawa mai ƙarfi da matakin da hukumar EFCCn ta ɗauka na rufe asusunta bisa zargin wasu kura-kuran kuɗi.

Gwamnatin Gwamna Ademola Adeleke ta ƙalubalanci EFCC da ta bayyana dokar da ta yi amfani da ita wajen ɗaukar matakin, tana mai cewa dole ne hukumar ta nuna yadda hukuncin da ta yanke ya yi daidai da dokokin Najeriya da kuma dokar da ta kafa hukumar.

Mene ne ainihin abin da ya faru?

A ranar 5 ga watan Agustan 2026, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta sanar da cewa ta sanya umarnin hana cire kuɗi (Post No Debit Order) kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, inda ta ce an ɗauki wannan mataki ne a matsayin wani ɓangare na binciken da take gudanarwa kan harkokin kuɗaɗen jihar.

Sai dai Gwamnatin Jihar Osun ta yi watsi da zarge-zargen da EFCC ta yi mata, tana mai jaddada cewa ba ta aikata wani laifi ba, tare da tambayar dokar da hukumar ta dogara da itawajen ɗaukar wannan mataki.

Masu sukar matakin da dama, tare da Gwamnatin Jihar Osun, sun yi ikirarin cewa matakin EFCC yana da nasaba da siyasa.

Gwamna Ademola Adeleke, wanda a baya-bayan nan ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar Accord Party, ya zargi hukumar da nuna goyon baya ga wasu mutane masu alaƙa da jam’iyyar APC mai mulki domin kawo cikas ga ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓe.

Adeleke ya jaddada cewa ana sa ran EFCC za ta gudanar da ayyukanta ba tare da nuna bambancin siyasa ba, kuma bai kamata ta bari siyasa ya yi tasiri kan yadda take sauke nauyin da doka ta ɗora mata ba.

Me dokar Najeriya ta ce kan matakin na EFCC?

Hukumar EFCC ta sanya wani umarni na “hana cire kuɗi” (Post No Debit Order) kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, matakin da ya haifar da muhawara da suka daga masu sa ido kan harkokin siyasa da masana shari’a da sauran masu ruwa da tsaki.

Masu sukar matakin sun rika aza ayar tambaya kan lokacin da aka ɗauke shi, suna mai nuni da cewa an yi hakan ne kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamnan jihar da ke tafe nan da wasu makonni.

Da dama sun bayyana cewa lamarin ya ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar akwai manufar siyasa a cikinsa, duk da cewa EFCC ta dage cewa matakan da take ɗauka suna da alaƙa ne kawai da nauyin da doka ta ɗora mata na binciken zarge-zargen laifuffukan kuɗi.

A yayin da cece-kucen ke ci gaba, an fara tayar da muhimman tambayoyi kan wace doka EFCC ta dogara da ita wajen ɗaukar wannan mataki da hanyoyin da doka ta tanada kafin a sanya umarnin hana cire kuɗi daga asusu, da kuma ko irin wannan iko na iya shafar asusun gwamnatin jiha.

BBC ta yi duba kan muhimman bayanan da suka shafi lamarin da hujjojin da ɓangarorin biyu ke gabatarwa, da kuma abin da masana shari’a da masu sharhi kan harkokin jama’a ke cewa game da sahihancin matakin EFCC a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Mene ne ‘rufe asusun banki’ kuma ya halasta?

Umarnin hana cire kuɗi (Post No Debit Order) wani takunkumi ne da ake sanyawa kan asusun banki wanda ke hana cire kuɗi ko tura su zuwa wani asusu har sai an janye umarnin.

Da yake magana da BBC, Barista Joe Onyeabor, lauya mai zaman kansa da ke zaune a Jihar Enugu kuma tsohon jami’in hulɗa da jama’a na Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) a jihar, ya ce Dokar EFCC ta bai wa hukumar ikon neman a sanya umarnin hana cire kuɗi kan asusun banki yayin da take gudanar da bincike kan zargin laifuffukan kuɗi.

A cewarsa, duk da haka, wajibi ne hukumar ta bi matakan shari’a da suka dace kafin ta ɗauki irin wannan mataki, ciki har da samun izinin kotu da ake buƙata.

Ya ƙara da cewa Dokar EFCC ba ta bayyana ƙarara ko za a iya sanya irin wannan umarni kan asusun bankunan gwamnatin jiha ba.

A ra’ayinsa, dokar ta fi magana ne kan asusun wani “mutum”, kuma ba ta fito fili ta tanadi rufe asusun bankunan gwamnatin jiha ba.

Kodayake ya amince cewa EFCC na iya fassara kalmar “mutum” ta yadda za ta haɗa da gwamnatin jiha, Onyeabor ya ce sahihancin irin wannan fassara abu ne da a ƙarshe kotu ce za ta yanke hukunci a kansa.

Zuwa wane lokaci doka ta bai wa EFCC damar rufe asusun banki?

A cewar kakakin EFCC, Dele Oyewale, hukumar yaƙi da cin hancin na da ikon rufe asusun banki yayin gudanar da bincike, kuma za ta iya ci gaba da sanya irin wannan takunkumi fiye da sa’o’i 72, ko da akwai umarnin kotu ko babu.

Da yake magana da BBC, Oyewale ya ce matakan da hukumar ke ɗauka suna bisa dokar binciken laifuffukan kuɗi da kuma hana motsa kuɗaɗen da ake zargin suna da alaƙa da haramtattun ayyuka.

Lokacin da aka tambaye shi abin da zai faru bayan cikar sa’o’i 72 ɗin, Oyewale ya ƙi bayar da cikakken bayani.

Abin da ya sa muka rufe asusun gwamnatin jihar Osun – EFCC

A cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta bayyana dalilan da suka sa ta sanya umarnin hana cire kuɗi (Post No Debit Order) kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, tana mai cewa tana binciken jihar tun daga watan Maris na shekarar 2026.

Hukumar ta yi zargin cewa ta gano wasu kura-kurai a yadda aka sarrafa kuɗaɗen gwamnatin jihar, ciki har da kuɗaɗen Asusun Muhalli (Ecology Fund) da Asusun Tallafi (Intervention Fund) da kuma asusun da jihar ke karɓar rabon kuɗaɗe daga Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC).

A cewar hukumar, ma’amalolin da take bincike sun shafi kusan naira biliyan 11.

Da take bayani kan dalilin rufe asusun, EFCC ta ce kasancewar binciken kaɗai bai isa ya sa ta sanya umarnin hana cire kuɗi ba.

Sai dai ta ce ta lura da wasu motsa kuɗaɗe da take ganin suna da alamar tuhuma daga asusun da abin ya shafa, waɗanda aka fara tun ranar 2 ga watan Agustan 2026.

Gwamnatin Osun ta musanta ɓarnatar da naira biliyan 11

Da take mayar da martani ga zarge-zargen na EFCC, gwamnatin Jihar ta musanta aikata wani laifi tare da yin watsi da ikirarin cewa an wawure naira biliyan 11, tana mai bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Oluomo Kolapo Alimi, ya fitar ya bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙoƙarin da ya gaza na kare wani matakin da ya saɓa wa doka ta hanyar jingina shi da zarge-zarge marasa tushe.”

Ya kuma yi zargin cewa rufe asusun bankunan jihar na da manufar siyasa, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa buƙatar tsohon gwamna Gboyega Oyetola domin hana gwamnatin jihar biyan tallafin rage ra

ɗaɗin halin matsin tattalin arziki da ta yi wa ma’aikata alƙawari.

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga PantamiGazawar Demarketing: Yadda Sukar Rarara Mai Cike da Kiyayya ga Pantami Ya Rushe Daga Yushau A. ShuaibƘungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin AikiDakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da suƳan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari'a da ke Jihar KatsinaBa ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe - INECJam'iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya SheƙaYan Bindiga Sun Kashe Kanal Abdussalam Ude Sun Raunata MatarsaMutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi Mataimakinsa
X whatsapp