Hukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh Jingir
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Najeriya ta yi Allah wadai da kalaman da malamin addini Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi, inda da ta ce za su rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna a tsakanain addinai.
Hukumar ta buƙaci Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar DSS da sauran hukumomin da abin ya shafa su kama tare da gurfanar da Sheikh Jingir kan zargin furta kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Shugaban hukumar, Tony Ojukwu a wata sanarwa, ya ce kalaman malamin, waɗanda suka yaɗu a wani bidiyo, suna yin kira ga siyasar wariya ga wasu addinai da kuma amfani da kalmar “kafirai”.
Ya ce hakan ya saɓa wa ƙa’idojin daidaito da zaman lafiya tsakanin ƴan Najeriya, kuma hakan na iya haddasa tashin hankula.
Hukumar ta kuma yi kira ga malamai, sarakuna da ‘yan siyasa da su guji kalaman rarrabuwar kawuna, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen zaɓen 2027.












