Home Taska Yadda Mutane 18 Suka Tsallake Rijiya da Baya a Jahar Kwara

Yadda Mutane 18 Suka Tsallake Rijiya da Baya a Jahar Kwara

Yadda Mutane 18 Suka Tsallake Rijiya da Baya a Jahar Kwara

Allah ya kawo wani lamarin wuta da sauki yayin da wata Motar Bus dake tsakar tafiya a kan titi makare da mutane ta kama da wuta.

Mutum 18 dake cikin motar sun samu nasarar tsira daga lamarin, amma kayan su baki ɗaya sun kone kurmus a ciki.

Kwamandan hukumar kare haɗurra na jihar Kwara ya ce dole ta sa suka tsayar da motoci a kan hanyar domin shawo kan wutar.

Kwara– Wasu mutane 18 sun ga tashin hankali kuma lamarin ya zo da sauƙi yayin da Motar Bus mai ɗaukar mutum 18 da suke ciki ta kama da wuta ta cikin zabga gudu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, lamarin wanda ya auku a ƙauyen Koko Araromi, kan hanyar Ajase Ipo, jihar Kwara ya bar matafiya da direbobi a tsaye.

Motar Bas ɗin, wacce rahoto ya nuna cewa tana kan hanyar zuwa garin Osdogbo a jihar Osun ta kama da wuta ne da misalin ƙarfe 10:57 na safe ana cikin zabga tafiya.

Allah ya kawo abun da sauki, domin duk da ba’a rasa rayuka ba kasancewar Mutanen cikin motar sun yi gaggawar fita, amma duk kan kayan su da suke tafe da su a motar sun kone kurmus.

Wane matakin hukumomi suka ɗauka?

Shugaban rundunar hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a wata hira ta wayar salula.

Owoade wanda ya alaƙanta kama wutar motar da yoyon man Fetur ɗin motar, ya bayyana cewa:

“Jami’an hukumar kare haɗurra FRSC sun ɗauki matakin dakatar da motoci masu tafiya a kan hanyar na tsawon mintuna saboda wutar dake ci a Bas ɗin, hakan ya zame musu wajibi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp