Home WASANNI Arsenal da Newcastle na Zawarcin ‘Dan Wasan AC Milan da Portugal Rafael...

Arsenal da Newcastle na Zawarcin ‘Dan Wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao

Arsenal da Newcastle na Zawarcin ‘Dan Wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao

Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan gaban Chelsea Armando Broja, mai shekara 20. A halin yanzu dan wasan na Albania yana zaman aro ne a Southampton. (Football in London)

Chelsea ta ba da fifiko kan sayen dan wasan bayan Sevilla da Faransa Jules Kounde, mai shekara 23, a bazara, yayin da Blues kuma ke son dauko dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila Declan Rice, mai shekara 23, da kuma dan wasan tsakiyar Monaco mai shekara 22 Aurelien Tchouameni. (Telegraph)

Kocin Leicester Brendan Rodgers ya ce dole ne su yi tunani game da makomar dan wasan tsakiyar Belgium Youri Tielemans, mai shekara 24, wanda ya shiga watanni 18 na karshen kwantiraginsa, a dai-dai lokacin da Arsenal da Manchester United ke sha’awarsa (Metro).

Kofar Juventus a bude take, don sayen dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 26, da dan wasan baya na Brazil Alex Sandro, mai shekara 31. (Gazzetta dello Sport).

Barcelona na fatan ganin ta dakile zawarcin dan wasan tsakiyar Spain Gavi, mai shekara 17, da dan wasan bayan Uruguay Ronald Araujo, ta hanyar sabunta kwantiragin ‘yan wasan biyu. Liverpool da Manchester United duk suna zawarcin Araujo mai shekaru 22. (ESPN)

Arsenal da Newcastle na zawarcin dan wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao, mai shekara 22 a bazara. (Fichajes)

Pep Guardiola yana son Raheem Sterling, mai shekara 27, ya rattaba hannu kan sabon kwantaragi a Manchester City amma ya ce kungiyar za ta yanke shawara ta karshe kan makomar dan wasan na Ingila. Yarjejeniyar Sterling za ta kare ne a watan Yunin 2023 kuma ya ce a shirye yake ya koma wata kasar don ci gaba da buga wasanni (Independent)

Mauricio Pochettino na tunanin barin Paris St-Germain a bazarar nan bayan da ya samu sabani da manyan jiga-jigan kungiyar. (Goal)

Manchester United na sha’awar sayen dan wasan bayan Borussia Monchengladbach Ramy Bensebaini, mai shekara 26, kuma suna kallon dan wasan na Algeria a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan bayan Ingila na hagu Luke Shaw. (Fichajes)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp