Home Labarai Shin da Gaske Tsohon Sarki Sanusi II Zai Kawo Ziyara Jahar Kano...

Shin da Gaske Tsohon Sarki Sanusi II Zai Kawo Ziyara Jahar Kano ?

Shin da Gaske Tsohon Sarki Sanusi II Zai Kawo Ziyara Jahar Kano ?

Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.

Ana gani abubuwa da dama ka iya ta da zaune tsaye tsakanin al’ummar Kano, matukar Sanusi II ya shigo jihar kano.

Kano – Masana a siyasa da tsaro sun nuna matukar damuwarsu kan shirin tsohon sarkin da aka sauke, Sanusi Lamido, na kai ziyara jahar Kano.

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jiha, waɗan da suka zanta da jaridar Leadership, sun roki tsohon sarkin ya dakatar da shirin zuwa Kano a halin yanzu.

A cewarsu, tsoron da suke shi ne, akwai yuwuwar tada hankulan mutane wanda ka iya sanadin rikici tsakanin masoyan tsohon sarkin da yan adawarsa.

Ɗaya daga cikin manyan mutane, kuma babban jami’in tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa yace ra’ayin tsohon sarkin na kai takara Kudu ya fusata wasu kuma zasu iya amfani da zuwansa don tada rikici.

Kazalika ya ƙara da cewa duk da sanin kowa ne an tunɓuke shi daga Sarauta, amma yana halartar taruka cikin kayan Sarauta, hakan ka iya jawo matsala saboda akwai Sarki mai ci a Kano.

Ya ce:

“Kowa ya san cewa Sanusi tsohon ɗalibin Kwalejin Legas ne, kuma yana da abokan da suka yi makaranta tare a kudu maso yamma, amma har yanzun ba’a san wanda yake goyon bayan ya gaji Buhari daga yankin ba.”

“Kazalika sanin kowa ne Sanusi ya bayyana cewa ya fi son rike muƙamin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, fiye da shiga neman kujerar siyasa.”

Shin gwamnatin Kano ta san da zuwan tsohon sarkin?

A ɓagaren gwamnati, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace ba shi da masaniya kan shirin zuwan Sanusi.

Ya ƙara da cewa idan ma jita-jitar gaskiya ce, “Muna maraba da shi, a matsayinsa na.ɗan asalin jihar Kano, yana da damar zuwa jiharsa, gwamnati ba ta da matsala da haka.”

Tsohon hadimin Sanusi, Farfesa Auwal Hamisu Yadudu, ya bayyana cewa ba shi da masaniyar zuwan tsohon sarkin Kano.

Farfesa Yadudu yace:

“Ban san zai shigo jihar Kano ba, ba wanda ya sanar da ni wannan shirin, kuma ina da yaƙinin cewa idan zai shigo ina daga cikin waɗan da za’a gaya wa.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp