ITU Ta nada Pantami Matsayin Jagora a Taron ta na Duniya a kasar Switzerland

Kungiyar Sadarwa ta Kasa da Kasa wato International Telecommunication Union (ITU) ta nada Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin shugaban taron kolin kingiyar da gudana a shalkwatar kungiyar dake Geneva a kasar Switzerland.

Kungiyar Ta ITU ta tabbatar da nadin na Pantami ta cikin wata wasika mai dauke da sa hannun babban sakatern ta, wanda ya bayyana cewa kungiyar ta nada Farfesa Pantami matsayin shugaban taron kolin ta.

”Bisa la’akari da sadaukarwarsa ga kungiya, da kuma rawar da yake takawa a cikin tsare tsaren gudanar da taron na WSIS” masu ruwa da tsaki sunga dacewar nadashi bisa wannan matsayi, taron zai sami halartar manyan ministoci daga kasashen dake cikin wannan kungiya.

Dandalin taron na WSIS 2022 na matsayin babban dandalin tattaunawa gami da rawar da hanyoyin sadarwa ke takawa, kuma tana matsayin hanyar aiwatar da manufofin cigaba mai dorewa, bisa la’akari da tsarin da duniya ke kai gami da bibiyar hanyoyin aiwatar da kudirin cigaba mai dorewa zuwa shekarar 2030 na (UNGA Resolution A/&70/1).

Haka zalika dandamalin na WSIS na bin diddigin nasarorin da ake samu bisa hadin Gwiwar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa, ta hanayar samar da bayanan binciken da suka gudanar.

Taron na WSIS, na kungiyar ITU da asusun tallafawa kananan yar ana majalisar dinkin duniyar da UNCTAD suka shirya tare da hadin wasu hukumomin majalisar dinkin duniyar guda 24, da suka hadar da FAO, ILO, ITC, UNDESA, UNICO, UNITAR, UNHCR, UNODC, UNEP, UPU, UN TECH BANK, WMO, WIPO, WHO, WFP da dai sauransu.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 11 minutes 51 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 53 minutes 16 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com