Home Labarai Rundunar Farar Hula ta Kashe ‘Yan Bindiga 9, ta Kama 5 a...

Rundunar Farar Hula ta Kashe ‘Yan Bindiga 9, ta Kama 5 a Katsina

Rundunar Farar Hula ta Kashe ‘Yan Bindiga 9, ta Kama 5 a Katsina

 

A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan kungiyar Civilian Joint Task Force suka dakile wani hari da suka kai wani gari a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina tare da kashe wasu ‘yan ta’adda biyu.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma cafke wasu ‘yan ta’adda biyar tare da kame babura tara da aka yi amfani da su wajen kai harin.

Wasu majiyoyi da suka zanta da wakilinmu sun ce ‘yan ta’addan sun kai hari garin ne da misalin karfe 4:30 na yamma, inda suka ce ‘yan ta’addan sun mamaye garin ne a cikin babura akalla 10.

A yayin farmakin, tawagar da ke yaki da ‘yan ta’addan sun yi arangama da ‘yan ta’addan, kuma a yayin musayar wuta da bindiga, sun kashe mutane tara da ake zargi.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ta kama wasu ‘yan kungiyar su biyar a yayin samamen.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce har yanzu DPO da ke yankin bai yi wa rundunar bayanin faruwar lamarin ba.

Isah ya ce, “Zan yi muku bayani a duk lokacin da DPO na yankin ya sanar da hukumar game da lamarin.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp