Hukumar DSS ta bukaci Al’ummar Nijeriya su gudanar da Shagulgulan Karshen shekara cikin lumana

Gabatowar bukuKuwan Kirsimeti da karshen shekara hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya, ta bukaci Al’ummar kasar da su gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da bin doka da Oda.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar na kasa Peter Afunanya, Ph.D, fsi Ya sanyawa hannu, mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Disambar 2022, aka raba ga manema labarai a birnin Abuja.
Hukumar tace zata hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da doka da Oda, don haka tana kira ga Al’umma, Malamai da ‘yan siyasa, shuwagabanni da Suyi wa’azuzzuka ko jawabai Da zasu tabbatar da zaman lafiya, samar da hadin kai, gami da wayar da kan mabiyan su hanyoyin da zasu kare kansu a yayin bukukuwan.
Wannan shi yafi dacewa kasancewar kada wasu suyi amfani da damar wajen tada zaune tsaye.
Hakazalika ‘yan siyasa a yayin da suke yakin neman zabe, ana so su gudanar cikin ka’ida, ya kamata su nisan ci labaran karya, kalaman kyama, tashin hankali da dukkan Abubuwan da zasu kassara tsaron kasa.
Haka kuma sanarwar ta bukaci ‘yan kasuwa dasu gujewa dabi’un da zasu haifar da hauhawar farashin maras fa’ida, kagar karancin samfuran kayayyaki abun da ka iya haifar da tashin hankali ta hanyar jifa Al’umma cikin halin rashin tabbas.
Hukumar ta kuma bukaci ‘yan Jarida da kungiyoyi masu zaman kansu da su kasance masu kishin kasa a yayin gudanar da ayyukan su matsayin su na masu ruwa da tsaki a fannin gina kasa da godabar da harkokin tsaron ta.
Daga Bisani shugaban Hukumar Alhaji Y. M Bichi, CFR, fwc a madadin jami’an hukumar yana Fatan Al’ummar zasu gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali tare da tayasu murnar sabuwar shekara

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 16 hours 49 minutes 3 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 30 minutes 28 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com