Bikin Kirsimati da Sabuwar Shekara: FRSC zata girke jami’ai sama da Dubu 36 a Sassa Nijeriya
Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya FRSC, ta sanar da aike jami’anta a sassa daban-daban na kasar domin gudanar da sintiri a tituna yayin gudanar da bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara da ke tafe.
Wannan na cikin jawabin da mukaddashin shugaban hukumar , Dauda Biu ya yi a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Litinin, ya ce sun tanadi jami’ai 36,224 da za su yi wannan aikin.
Read Also:
Sai dai ya ce hukumar na bai wa ‘yan Najeriya tabbacin kare lafiyarsu da dukiya a lokacin da ake gudanar da bukukuwan na karshen shekarar 2022 lafiya da fatan ganin 2023 da ke tafe.
A Najeriya dai ana yawan samun hadurran motoci a manya da kananan titunan kasar, musamman lokacin bukukuwan karshen shekara.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasar da ‘yan sanda na dora alhakin hadurran ababen hawan kan tukin ganganci, ko gudu fiye da kima da direbobi ke yi, sai kuma rashin hakurin masu ababen hawa a lokacin da aka samu cunkoun ababen hawa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 21 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 20 hours 2 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com