Home Labarai Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya dasu karbi kudin zabe idan an basu

Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya dasu karbi kudin zabe idan an basu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar kasar da su karbi kudaden da ‘yan siyasa suke rabawa lokacin zabe, amma kuma su zabi abinda suke so.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan kada kuri’ar sa a zaben gwamnan jihar Katsina da na ‘yan majalisu, shugaban ya ce yana da yakinin jam’iyyarsa ta APC za ta sake samun nasara.

Shugaban ya ce ko kadan bai yi mamakin yadda sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu ya kaya ba, wanda aka bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara.

Buhari ya ce Jam’iyyar APC ta gudanar da yakin neman zabe tukuru wajen bayyana manufofinta da shirin da take da shi ga jama’ar Najeriya.

Shugaban yace duk da yadda matsalar karancin kudi ta yiwa shirin sayen kuri’u dabaibayi, har yanzu wasu bata garin ‘yan siyasa na rabawa masu zabe kudade.

Buhari ya bai wa jama’a shawarar cewar su karbi kudinsu soke, kana su zabi abinda suke so.

Daga karshe shugaban ya jinjinawa ‘yan Najeriya akan amincewar da suka yi wa jam’iyyar su, yayin da su kuma suka saka musu wajen gudanar da ayyuka a bangaren ilimi da kula da lafiya da kuma gina kayan more rayuwa.

Shugaban ya kuma yabawa kafofin yada labarai saboda rawar da suka taka wajen wayar da kan jama’a domin zabin irin shugabannin da suke so da kuma tuhumarsu idan sun saba alkawarin da suka musu.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp