Zababben gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya nada tsohon shugaban hukumar lura da jami’oin Nijeriya (Tetfund) Dr. Baffa bichi matsayin shugaban kwamitin karbar Mulki.
Wannan na kunshe ne cikin watan sanarwa da sakataren yada labaran zababben Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar wadda aka raba ga manema labarai a yammacin juma’a.
Inda Sanarwar ta bayyana cewa biyo bayan tabbatar masa da shaidar kasancewar s ana zababben gwamnan jihar kano Abba Kabir yusuf ya nada kwamitin karbar Mulki daga hannun gwamanti mai shudewa.
Read Also:
Inda tsohon sakataren hukumar ta tetfund kuma wanda ya yiwa jam’iyyar NNPP takarar sanata a santoriyar kano ta arewa a zaben 2023, Dr. Baffa Bichi matsayin shugaban kwamitin karbar mulkin Abdullahi Musa matsayi sakatare.
Aikin Kwamitin shine gudanar da ayyukan mika mulki cikin tsari daga gwamnatin Ganduje mai barin gado zuwa gwamnatin Abba Gida Gida mai jiran gado.
Mai girma Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado zai kaddamar da kwamitin a ranar Asabar 1 ga Afrilu, 2023 da karfe 2:00 na rana. Haka kuma akwai cikakken jerin membobin Babban Kwamiti, yayin da za a sanar da ƙananan kwamitoci a sassa daban-daban.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 9 hours 30 minutes 13 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 11 minutes 38 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com