Home Labarai Majalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka...

Majalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai Kwara

Bayan umarnin tura wata bataliyar soji zuwa sassan jihar Kwara, sakamakon mummunan harin da ya yi sanadiyyar kisan sama da mutane 160 a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawa da Gwamnan Jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da yammacin Alhamis.

Shugaba Tinubu a wata sanarwa da mai taimaka masa a fannin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar cikin daren Laraba ya kuma naɗa kwamandan da zai jagoranci rundunar sojin da za a tura jihar Kwara, wadda za ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya da aka yi wa laƙabi da ‘Operation Savanna Shield’.

A bangare data, Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kashe-kashen  mutane a jihohin Katsina da Kwara da kuma Benue, inda suka kwatanta lamarin a matsayin kololuwar rashin imani.

Cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis, shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Malam Inuwa Yahaya ya bayyana kaɗuwarsa kan rayukan da aka rasa, inda ya miƙa sakon ta’aziyya a madadin sauraran gwamnonin zuwa ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma al’ummar jihohin uku.

Majalisar Dinkin Duniya da kasar Turkiyya sun yi Alla-wadai da kisan gillar, da aka yi a jihar Kwara, yayin da ‘yan majalisar dattawa da suka fito daga arewancin Najeriya suka bukaci a yi gagarumin garambawul a fannin tsaro.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce ƙasar ta yi matukar bakin ciki da asarar rayukan da aka samu sakamakon harin ta’addanci.

“Muna Allah wadai da wannan mummunan harin kuma muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma al’ummar Najeriya

Sanarwar ta ƙara da cewa, Turkiya za ta ci gaba da tallafawa Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci.

Tinubu ya ziyarci Turkiyya a makon da ya gabata don ziyarar aiki.

A lokacin ziyarar da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kai Turkiyya kwanan nan sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi tara don karfafa dangantakar ƙasashen biyu, ciki harda haɗin gwiwa a ɓangaren tsaro.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a ranar 3 ga watan Fabrairu, a Jihar Kwara.

Sakataren ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma jama’a da gwamnatin Najeriya. Yana fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Sakataren ya sake nanata haɗin kan Majalisar Dinkin Duniya da Gwamnati da al’ummar Najeriya a ƙoƙarin da suke yi na yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, sannan ya jaddada muhimmancin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp