Karo na Biyu: Shugaba Buhari ya ɗage Kidayar 2023

President-Muhammadu-Buhari

Karo na Biyu: Shugaba Buhari ya ɗage Kidayar 2023

A karo na biyu, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ɗage kidayar 2023 da aka shirya gudanarwa a Najeriya.

Ya ɗauki wannan matakin ne bayan ganawa da shugaban NPC na ƙasa, Nasir Isa-Kwarra, da tawagarsa a fadar shugaban ƙasa.

A halin yanzun, Buhari ya bar wuƙa da nama hannun gwamnati mai zuwa karƙaashin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sake ɗaga aiki kidayar mutane da gidaje a Najeriya na shekarar 2023.

Jaridar ta ce shugaban ƙasan ya ɗage aikin kidayar wanda aka tsara gudanarwa ranar 3 zuwa 7 ga watan Mayu, 2023, a yanzu ya bar wuƙa da nama hannun sabuwar gwamnati.

Buhari ya ɗauki wannan matakin ne a wurin ganawa da wasu mambobin majalisar zartaswa da shugaban hukumar kidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Isa-Kwarra, da tawagarsa a Abuja ranar Jummu’a.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai da safiyar Asabar mai ɗauke da sa hannun Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed.

Sanarwan ta ce:

“Yayin da aka cimma matsayar sake ɗage aikin kidayar, taron ya kara jaddada muhimmancin kidayar yan Najeriya da gidaje, shekaru 17 bayan gudanar da kidaya a Najeriya.”

“Hakan ne kaɗai zai sa a tattara bayanai waɗanda zasu taimaka wajen cika burin kawo ci gaba a ƙasar nan kuma ya daidaita walwaha a rayuwar mazauna Najeriya.”

A wurin taron, an ji shugaba Muhammadu Buhari na cewa an cimma nasarori masu yawa a shirye-shiryen gudanar da kidaya, wacce aka ɗaga yanzu.

Ya kuma yaba wa hukumar kidaya ta ƙasa NPC bisa yadda ta ɗauki tsaruka da hanyoyin gudanar da sahihiyar kidaya wacce za’a dogara da ita a gwamnatance.

Jiga-jigan da suka halarci zaman Manyan kusoshin gwamnati da suka je wurin taron sun kunshi, Antoni Janar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed.

Sauran su ne, ƙaramin ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Mista Clem Agba, da kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 35 minutes 13 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 16 minutes 38 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com