Ba za mu bar tsibirin Tafkin Chadi ko daya a hannun ‘yan ta’adda ba – MNJTF

Kwamandan rundunar sojin hadin gwiwar da ke yaki da ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chinuisi, ya bayyana aniyarsa ta ganin sun murkushe duk mayakan Boko Haram da na ISWAP da ke zama a tsibiran da suke kewaye da tafkin baki daya.

Janar Chinuisi ya bayyana haka ne, lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a Balangoua da ke kasar Kamaru, da kuma Bagasola da Bibi da ke cikin kasar Chadi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar ta MNJTF, laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya ce Kwamandan ya bayyana karara cewar, ya  kai ziyarar ce domin tantance karfin rundunonin da ke bakin aiki daga da kuma karfafa musu guiwa wajen ganin sun cigaba da jajircewa a yakin da suke gwabzawa, yayin da ya yi musu alkawarin taimakon da suke bukata domin samun nasara.

Kanal Abdullahi ya ce kafa rundunar MNJTF ta taka rawa gaya wajen dakile kaifin mayakan Boko Haram wajen shirya kai hari a tsibiran da ke Tafkin Chadi da ake kira Tumbus, yayin da janar Chibuisi ya bukaci sojojin da suk dada kara kaimi wajen dorawa akan nasarorin da suka samu, domin kawar da mayakan daga tsibirin.

Ziyarar aikin ta Kamaru da Chadi na zuwa ne kwana guda bayan kammala irinta da Kwamandan ya kai Malam Fatori da ke Najeriya da kuma Diffa da Bosso a Jamhuriyar Nijar, a kokarin da sojojin ke yi na kawar da ayyukan ta’adddanci a yankin Tafkin Chadi baki daya domin mayar da zaman lafiya..

Kanal Abdullahi ya ce Janar Chibuisi ya sha alwashin bai wa dakarun goyon bayan da suke bukata domin samun nasarar yakin baki daya.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 29 minutes 53 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 11 minutes 18 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com