Rahotanni na bayyana cewa Tsohon Gwamnan Jihar Yobe Sanata Bukar Abba Ibrahim ya rasu yana da shekara 73, ya rasu ne a ƙasar Saudiyya bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Kafin rasuwarsa ya kasance Gwamnan Jihar Yobe daga 1992 zuwa 1993, sannan ya sake jagorantar jihar a matsayin gwamna tun daga 1999 har zuwa 2007.
Marigayin ya wakilci Jihar Yobe a Majalisar Dattawan Nijeriya daga 2007 har zuwa 2019.
Read Also:
Bukar Abba ya yayi karatun firamare a 1957. inda a 1965, ya tafi Kwalejin gwamnati ta Maiduguri domin ci gaba da karatun sakandare. Marigayin ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello a 1972 inda ya samu digiri kan Quantity Surveying.
Bayan nan sai ya ci gaba da digirinsa na biyu a Birtaniya tsakanin 1981 zuwa 1982.
Daga 1985 zuwa 1988 ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnatin jihar Borno inda har ya kai matakin kwamishinan ayyuka.
A Disambar 1991 watanni bayan Yobe ta samu jiha sai ya yi takarar gwamna inda ya ci zabe karkashin jam’iyyar SDP. Ya rike wannan mukamin har zuwa lokacin da sojoji suka kwace iko da gwamnatin.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 36 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 17 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com