Fadar shugaban Nijeriya ta ce umarnin bude iyakokin kasar da jamhuriyar Nijar da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar, ba wai yana nufin bada damar shigo da kayan masarufi da sauran kayayyakin da tsohuwar gwamnatin Buhari ta hana shigo da su kasar ba ne.
”Wannan umarnin yana magana ne kawai akan abubunwan da suka faru ko matakan da ECOWAS ta dauka na sanyawa ƙasar Nijar takunkumi sakamakon Juyin mulki da sojojin kasar suka yi, don haka umarnin shugaban kasar yana magana ne kawai a koma Inda ake a bara “.
Babban Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana hakan, yayin da yake Karin bayani ga manema labarai ta wayar tarho dangane da umarnin da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar na bude iyakokin Nigeria da jamhoriyar Nijar.
Read Also:
Yace umarnin ba wai yana nufin a cigaba da shigo da kayan masarufi da sauransu ba ne, “dokokin mu na cikin gida na hukumar kwastam suna nan kuma jami’an hukumar zasu cigaba sa sanya idanu akan duk kayan da za’a Shigo da su Nijeriya.
”Kamar yadda aka sani a dokokin hukumar Kwastam akwai kayan da aka aminta da su akwai kuma wadanda ba’a aminta a shigo da su ba, don haka dokar da aka sa a baya tana nan tana aiki musamman akan shinkafa da wasu sauran abubuwan amfani na yau da kullum har yanzu dokar tana nan tana aiki aka su”.
Idan za’a iya tunawa tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari shi ne ya rufe iyakokin kasar inda aka hana shigo da Shinkafa, kayan masarufi da sauransu da nufin inganta wadanda ake samar wa a cikin gida Nigeria.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 44 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 25 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com