Janye Tallafin Lantarki ka iya jefa ‘yan Nijeriya mawuyacin hali

Al’ummar Najeriya za su fuskanci karin kudin lantarki muddin gwamnati ta ci gaba a kan shirinta na janye tallafi da kashi 15 cikin 100.

Yin hakan zai kara jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali bisa la’akari da hakin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

A ranar Talata ne mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya sanar da shirin gwamnatin, yana mai cewa za a yi hakan ne domin a rage kashe kudaden gwamnati.

Idan aka dauki wannan mataki za a rage kashe kudaden gwamnati da kusan dala biliyan biyu da miliyan dari shida.

Ba dai a bayyana lokacin da gwamnati za ta janye tallafin kashi 15 cikin 100 ba.

Ko a yanzu ma ba kowa ba ne yake iya sayen wutar saboda yadda ta yi tsada duk da cewa farashin ya banbanta daga gari zuwa gari da kuma atsakanin unguwanni.

Cire wannan tallafi na nufin wuta za ta koma hannun ‘yan kasuwa kacokan. To sai dai har kawo yanzu kusan fiye da kaso 70 na ‘yan Najeriya ba su da mitar da ake sanyawa kudi.

A kwanakin baya ne dai asusun lamuni na duniya ya shawarci Najeriya da ta cire tallafin mai kacokan da kuma tallafin da take bai wa ‘yan kasar a wutar lantarki.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 25 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 6 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com