Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2023 da ta gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da yunkurin gwamnatin jam’iyyar APC mai mulkin karkashin jagorancin Bola Tinubu, na murkushe yancin yada labarai da kafafen yada labarai ke da shi kundin tsarin mulki kasa na 1999 da aka yiwa gyaran fuska.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Alhaji Atiku Abubakar ya fitar kuma aka raba ga manema labarai. inda tace da ayyana yunkurin gwamnatin matsayin wata barazana ga harkokin yada labarai.
Read Also:
Atiku Ya yi kira ga yan jarida a kasar da cewa kada su bari wannan barazanar ta tsorata su, ta yadda zasu kasa sanar da al’umma rawar da gwamnatin da ke mulkinsu ke takawa wajen tasarrafi da al’amuran da suka shafi rayuwar su da walwalar su.
Idan za’a iya tunawa gwamnatin tarayyar Nijeriya na shan suka tun bayan da jaridar Daily Trust ta wallafa labarin kan batun yarjejeniyar Samoa da gwamantin Nijeriya, wadda ake zargin cewa akwai batun auren jinsi a cikin ta.
Lamarin da yasa gwamnatin tarayyar ta musanta, har ma ya ti barazanar daukar matakin Shari’a kan Kamfanin jaridar Daily Trust.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 46 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 28 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com