Babbar kotun jaha mai lamba 7 karƙashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu, ta tabbatar da ingancin dokar da majalisar jihar Kano ta samar wadda ta rushe sarakuna biyar da aka samar a cikin tsohowar doka.
Kotun ta ayyana cewar dokar masarautu ta shekarar 2024, wadda majalisar dokokin kano ta samar a matsayin dai-dai.
Da take yanke hukuncin a zaman ta na yau, kotun ta kuma bayyana cewar aikin majalisar dokoki shine ta yi doka, ko ta rushe doka, ko kuma ta yiwa doka gyaran fuska.
Read Also:
Mai shari’a Amina Adamu, ta kuma bayyana cewar Sarakunan Kano waɗanda gwamnati ta cire kada su kara kiran kansu a matsayin sarakuna, kuma su dawo da dukkanin wata kadara mallakin gwamnati wadda take hannunsu.
Tun da fari gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar inda ta roki kotun da ta tabbatar da dokar majalisa ta 2024.
Majalisar dokokin Kano dai ta yi wa dokar masarautu gyaran fuska wanda hakan ya dawo da masarauta guda ɗaya a jahar Kano.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 35 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 16 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com