Gwamnatin Kano ta Kaddamar da kwamitin mafi karancin Albashi

Gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na kasa, sa’o’i 48 kacal bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 kamar yadda suka cimma matsaya da kungiyar kwadago.

Wannan na cikin wata sanarwa da maigana da yawun Mataimakin Gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu ya fitar, wadda ta bayyana cewa Gwamna Yusuf ya jaddada alhakin kwamitin na tsara yadda ya kamata kan sabon mafi karancin albashin da aka amince da shi da kuma gabatar da shawarwari kan yadda gwamnatin jihar zata aiwatar.

Kano ita ce jiha ta farko a fadin kasar nan da ta fara kafa irin wannan kwamiti. An gudanar da bikin kaddamar da kwamitin ne a yau a fadar gwamnatin jihar, wanda mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranta a madadin gwamnan.

Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa aiwatar da sabon mafi karancin albashin zai kara habaka cigaban jihar Kano a dukkanin bangarori, domin jin dadin ma’aikata shi ne abin da gwamnati ta sa gaba.

An dai baiwa kwamitin makonni uku domin ya gabatar da rahotonsa. Gwamnan ya tunatar da ‘yan kwamitin cewa an zabe su bisa cancanta, ya kuma bukace su da su bayar da gamsassun sakamako.

Mambobin kwamitin sun hada da:

– Alh. Usman Bala Muhammad, mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin jiha (Shugaba)

– Alh. Ibrahim Jibril Fagge, Hon. Kwamishinan Kudi

– Alh. Musa Suleman Shanono, Hon. Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi

– Baba Halilu Dantiye, Hon. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida

– Baffa Sani Gaya

– Prof. Aliyu Isa Aliyu

– Salahudeen Habib Isa

– Ibrahim I. Boyi

– Ibrahim Muhammad Kabara

– Mustapha Nuraddeen Muhammad

– Abdulkadir Abdussalam

– Umar Muhammad Jalo

– Hassan Salisu Kofar Mata

– Yahaya Umar

Sabon shugaban kwamitin Alh.Usman Bala Muhammad, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin cikin gida ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar bisa amincewar da ta yi wajen zabo yan kwamitin.

Ya ba da tabbacin zasu yi aiki tukuru domin sauke nauyin da gwamnan jihar kano ya dora musu.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 17 minutes 32 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 58 minutes 57 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com