Home Labarai Ta kashe mijinta mai cutar shanyewar ɓarin jiki, ta jefar da gawarsa...

Ta kashe mijinta mai cutar shanyewar ɓarin jiki, ta jefar da gawarsa a kango

Ana zargin wata mata mai suna Rahimat Salaum da kashe mijinta mai fama da larurar shanyewar ɓarin jiki sannan ta jefar da gawarsa a cikin wani kango.

Lamarin ya faru ne a yankin Pegi da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kakakin rundunar ’yan sanda ta shiyyar Abuja, SP Josephine Adeh, ita ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Talata.

Ta ce tuni jami’an rundunar da ke yankin na Pegi ne suka cafke Rahimat a ranar Litinin.

A cewar Josephine, an kama matar ne lokacin da take ƙoƙarin tserewa da kayayyakin mijin nata, kafin ’yan sanda su yi mata ƙofar-rago su kama ta.

“Bayan an yi mata tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ita ce ta kashe mijin nata bayan wata sa’insa da ta shiga tsakaninsu. Daga nan ne ta yi wa jami’anmu jagora zuwa kangon da ta jefar da gawar tasa, inda aka tarar da shi ya yi mummunar ƙonewa,” in ji Kakakin ’yan sandan.

Sai dai ta ce ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma da zarar sun kammala za su miƙa ta gaban kotu domin ta girbi abin da ta shuka.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp