Home Labarai Majalisar Addinai a Nijeriya ta bukaci a kawo karshen Zanga Zanga a...

Majalisar Addinai a Nijeriya ta bukaci a kawo karshen Zanga Zanga a kasar

Majalisar jagororin addinai ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar III, da shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) Archbishop Daniel Okoh sun yi kira da a gaggauta kawo ƙarshen zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da ke gudana a faɗin Najeriya.
Sun yi wannan kiran ne a yau Juma’a cikin wata sanarwa da suka sanyawa hannu tare da babban sakataren majalisar NIREC, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua.
“Majalisar NIREC ta lura da abubuwan da ke faruwa a ƙasar a halin yanzu. Zanga-zangar wanda aka faro cikin lumana a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 ta ɗauki wani salo na tashin hankali daga baya.
Sanarwar ta ƙara da cewa “A cikin ƴan sa’o’i kaɗan an yi asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon wannan mummunan yanayi.”
Majalisar ta amince da cewa ana fuskantar wahalhalu da dama a ƙasar amma ta ce tashin hankali ba shi ne mafita ba, inda ta ƙara da cewa hakan zai ƙara dagula halin da al’ummar ƙasar ke ciki.
“NIREC tana kira ga ƴan Najeriya da su janye wannan zanga-zangar su baiwa gwamnati damar wanke kanta.” In ji sanarwar
A ƙarshe NIREC ta buƙaci gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakai domin biyan buƙatun ƴan ƙasar.
PRNigeria hausa
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp