Home Labarai Mayakan boko haram 50 sun mika wuya ga Sojoji a jihar Borno

Mayakan boko haram 50 sun mika wuya ga Sojoji a jihar Borno

Nigerian Army

Dakarun sojojin kasan Nijeriya sun sami nasarar kama kwamandan kungiyar Boko, mai kai musu kaya da kuma wadanda suke hada baki, gami da mayakan kungiyar da suka mika wuya da iyalansu.

Haka kuma dakarun rundunar sun sami nasarar kwato wadanda mayakan kungiyar suka yi garkuwa da su a mabambanta maboyar su, haka kuma dakarun sun sami nasarar kwato wasu kayyaki da bata gari suka sace a yayin gudanar da zanga-zangar luma a kasar.

Rundunar sojojin tace a ranar 4 ga watan Agusta, 2024 bisa aiki da wasu bayanan sirri dake yi ta sami nasarar kama wasu kwamandojin mayakan kungiyar boko haram a jihar Borno, wadanda ke yunkurin kutsawa sansanin ‘yan gudun hijira dake Damasak a karamar hukumar Mobbar.

Wadanda ake zargin da suka hadar da Bana Yamode da babagana Usman, wanda suka yi ikirarin sun je sansanin ne domin ziyartar iyalen su, wadanda tun da fari dama su sukayi jagoranci kai hari a yankin.

Haka kuma dakarun sun sami nasara kama wadanda ake zargi da safarar kayayyaki guda biyu Mallam Mustapha Isma’il mai shekaru 49 da kuma Abdulmudalibi Haruna mai shekaru 30, tare da ceto wasu mutum biyu a yayin sumamen.

Haka kuma mayakan boko haram 50 da iyalansu sun mika wuya ga rundunar a kananan hukumomin Bama, Gwoza da Dikwa, wannan dai na zuwa ne bisa yunkurin dakarun sojojin na kakkabe mayakan na boko haram.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp